1 Tarihi 29:10-13
Yabo gare ka, Yahweh, * Allah na kakanmu Yakubu, * tun fil'azal har abada.
Girma da iko naka ne, Yahweh, * da daraja da nasara da ]aukaka.
Dukan abin da ke a sama da }asa naka ne, Yahweh, * da mulki da sarautar kome da kome.
Wadata da ]aukaka daga wajenka suke, * kai ne ke mulkin duk kome.
Daga hannunka ke }ar}o da iko, * daga hannunka ke girma da sarautar duk kome.
Yanzu, ya Allahnmu, muna gode maka, * muna yabon sunanka mai daraja.
1 Sama'ila 2:1-10
Zuciyata tana murna da Yahweh, * ina samun }arfi daga wurin Yahweh.
Ina yi wa ma}iyana dariya, * ina matu}ar murna domin ka taimake ni.
Babu wani mai tsarki kamar Yahweh, * babu Dutse kamar Allahnmu.
Kada ku }ara yin magana ta girman kai, * kada fahariya ta fito daga bakinka.
Gama Yahweh Allah ne masani, * Mai Iko ne wanda ke auna ayyuka.
An kakkarya bakan jarumai, * amma aka sa wa raunannu }arko.
{osassu suna wadago don abinci, * amma mayunwata ba su bukatar aiki.
Bakarariya ta haifi 'ya'ya bakwai, * amma mai yawan 'ya'ya ta rasa su.
Yahweh na kashewa, ya kuma rayar, * yana kai wa Shawol, ya ma jawo.
Yawheh na talautarwa, ya ma arzuta, * yana }as}antarwa, ya ma ]aukaka.
Yana ]aga matalauta daga }ura, * ya tā da mabukata daga wurin bola,
don ya zaunad da su tare da 'yan sarakuna, * ya ba su kursiyi mai daraja.
Domin harsassan duniya na Yahweh ne, * a kansu ya kafa duniya.
Yana lura da tafiyar masu bautarsa, * amma miyagu za su halaka a Duhu.
Domin ba }arfin mutum ke sa ya yi nasara ba, * Yahweh zai kakkarya masu yi masa tawaye.
Ma]aukaki zai tsautar daga sama, * Yahweh zai hukunta har iyakokin duniya.
Zai ba sarkinsa iko, * ya tā da }arfin shafaffen sarkinsa.
Daniyel 3:26-7,29,34-41
Yabo gare ka, Yahweh, Allah na kakanninmu, * sunanka ya cancanci yabo da ]aukaka har abada.
Gama kai mai adalci ne a duk abin da ka yi mana, * dukan ayyukanka na gaskiya ne.
Hanyoyinka kuma ba su da aibu, * ai, dukan shari'unka na zahiri ne...
Ai, ta zunubanmu da }in manufa ne, * muka bau]e maka.
Mun yi sa~o a kowane abu, * ba mu yi biyayya da dokokinka ba....
Don darajar sunan nan naka, * kada ka ba da mu kwatakwata, * kada ma ka zare yarjejeniyarka.
Kada ma ka janye jin}anka daga gunmu, * saboda Ibrahim }aunataccenka,
da kuma Isiyaku bawanka, * da mai tsarkin nan naka, Isra'ila,
wa]anda ka yi alkawari ta kansu, cewa * jikokinsu za su yi yawan gaske,
kamar taurarin sama, * ko rairayin da ke bakin teku.
Yanzu, Yahweh, mun fi sauran al'ummai salwanta, * an ma yi mana }as}anci kwanan nan a dukan duniya, * saboda zunubanmu ne kuwa.
A wannan lokaci ma ba mu da sarki ko annabi, ko shugaba, * ba hadayar }onawa, ko hadaya, ko baiko, ko turaren }onawa,
ba gun da za a mi}a hadaya a gabanka, * ta neman jin}ai.
Duk da haka, don muna da karyayyar zuciya da ruhun tuba, * sai ka kar~e mu.
Kamar dai yadda ka kar~i hadayun }onawa na raguna da na bajimai, * da kuma na 'ya'yan raguna masu ki~a dubbai bisa dubbai,
haka ma ka kar~i hadayarmu ta yau, * domin muna binka sau da }afa.
Gama duk wanda ya dogara gare ka, * ko ka]an ba zai kunyata ba.
Yanzu mun bi ka da dukan zuciya, * kanmu }asa, hannunmu baya, * muna neman fuskarka.
Daniyel 3:57-88,56
Maimaitawa: Ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
Ku yabi Yahweh, ayyukan Yahweh duka, * ku yabi Yahweh, mala'ikun Yahweh.
Ku yabi Yahweh, sammai da birbishin }asa, * ku yabi Yahweh, ruwayen birbishin duniya.
Ku yabi Yahweh, dukan ikokinsa, * ku yabi Yahweh, rana da wata masu haske.
Ku yabi Yahweh, taurarin sama, * ku yabi Yahweh, tsattsafi da ra~a.
Ku yabi Yahweh, iska da hadari, * ku yabi Yahweh, wuta da zafi.
Ku yabi Yahweh, jaura da sanyi, * ku yabi Yahweh, }an}ara da dusar }an}ara.
Ku yabi Yahweh, dare da rana, * ku yabi Yahweh, haske da duhu.
Ku yabi Yahweh, wal}iya da girgije, * ki yabi Yahweh, ya ke duniya.
Ku yabi Yahweh, duwatsu da tuddai, * ku yabi Yahweh, mabun}usa }asa.
Ku yabi Yahweh, ma~u~~ugan ruwa, * ku yabi Yahweh, tekuna da koguna.
Ku yabi Yahweh, kifaye manya da }anana, * ku yabi Yahweh, tsuntsayen sama.
Ku yabi Yahweh, dabbobin duniya, * ku yabi Yahweh, 'yan adan.
Ku yabi Yahweh, Isra'ilawa, * ku yabi Yahweh, firistocin Yahweh.
Ku yabi Yahweh, bayin Yahweh, * ku yabi Yahweh, masu halin adalci.
Ku yabi Yahweh, tsarkaka masu sanyin hali, * ku yabi Yahweh, Hananiya, da Azariya, da Mishayel.
Yabo ya tabbata gare ka a sararin sama, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Daniyel 3:52-57
Yabo gare ka, Yahweh, Allah na kakanninmu, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo ga tsattsarkan sunanka mai daraja, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo gare ka a Haikalin ]aukakarka mai tsarki, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo gare ka, a bisa kursiyinka, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo gare ka, wanda ke zaune a bisa kerubobi, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo gare ka, mai duba zurfin duniya, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Yabo gare ka a sararin sama, * a yabe ka, a girmama ka har abada.
Ku yabi Yahweh, ayyukan Yahweh, * ku yabe shi, ku girmama shi har abada.
Maimaitawar Shari'a 32:1-12
Ku saurara, ku sammai, zan yi magana, * bari duniya ta ji kalmar bakina.
Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama, * kalmata ta fa]o kamar ra~a,
kamar yayyafi a bisa ]anyar ciyawa, kamar ]i]]igar ruwa a bisa ganyaye.
Gama zan yi shelar sunan Yahweh. * Ku yabi girman Allahnmu!
Dutsen nan, aikinsa cikakke ne, * dukan hanyoyinsa masu adalci ne.
Allah mai aminci ne, baya yaudara, * mai adalci ne, mai kirki.
Sun aikata }eta a gabansa, * su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, * su muguwar tsara ce, karkatacciya.
Haka za ku sāka wa Yahweh, * ku wawaye marasa hikima.
Ba shi ne Ubanku, Mahaliccinku ba, * wanda ya yi ku, ya kuma kafa ku?
Ku fa tuna da kwanakin dā, * ku yi tunani a kan shekarun da suka wuce.
Ku tambayi mahaifanku, za su fa]a maku, * ku tambayi dattawanku, su za su gaya maku.
Sa'ad da Ma]aukaki ya ba al'ummai gādonsu, * sa'ad da ya raba 'yan adan,
ya auna iyakokin al'ummai, * don kowacensu ta sami ]an allahnta.
Amma Yahweh ya za~i Isra'ila don kansa, * Yakubu shi ne rabon gādonsa.
Ya same shi a cikin hamada, * a jeji mai rurin iskoki.
Ya kewaye shi, ya lura da shi, * ya kiyaye shi kamar }wayar ido.
Kamar gaggafar da ke lura da she}arta, * tana rufe 'ya'yanta,
haka ya mi}a fukafukansa, ya ]auke shi, * ya tafi da shi a kan fukafukansa.
Yahweh ne ka]ai ya bishe shi, * ba wani ba}on allah tare da shi.
Fitowa 15:1-4a,8-13,17-18
Zan raira wa}a ga Yahweh, * gama ya ci gawurtacciyar nasara.
Doki da mahayinsa * ya jefar cikin bahar.
Yahweh }arfina ne, ina yabonsa, * shi ne wanda ya cece ni.
Wannan ne Allahna, zan girmama shi, * Allah na kakana, zan ]aukaka shi.
Yahweh maya}i ne, * sunansa Yahweh.
Karusan Fira'auna da rundunarsa * ya jefar cikin bahar...
Da hucin lumfashin hancinka * ruwa ya tattaru.
Rigyawa ta tsaya kamar tudu, * zurfafan ruwaye suka daskare a tsakiyar bahar.
Magabcin ya ce, * "Zan bi, in kama su,
in kwashi ganima, * muradina a kansu zai biya,
zan zare takobina, * hannuna zai halaka su."
Ka hura iskarka, * bahar ta rufe su,
suka nutse kamar darma * cikin manyan ruwaye.
Yahweh, wanene kamarka cikin alloli? * wa ke kamarka cikin ]aukaka da tsarki?
Mai banrazana ta yin al'ajibai, * mai aikata mu'ujjiza.
Ka mi}a hannunka na dama, * }asa ta ha]iye su.
Amma da }aunarka ka ja gorar * jama'arka da ka fansa.
Ka bi da su da }arfinka * zuwa tsattsarkan mazauninka...
Za ka kawo su, ka dasa su * a kan dutsen da ka za~a,
wurin mazauninka, * wanda kai, Yahweh, ka kafa,
tsattsarkan wurinka, ya Ubangiji, * wanda hannuwanka suka yi.
Yahweh zai yi mulki * har abada abadin.
Ezekiyel 36:24-28
Ga abin da Ubangiji Yahweh ya fa]i: * "Zan kwaso ku daga cikin al'ummai,
in tattaro ku daga dukan }asashe, * in kawo ku cikin }asarku.
Zan yayyafa maku tsabtaccen ruwa, * za ku kuwa tsarkaka daga dukan }azantarku. * Zan tsarkake ku daga dukan gumakanku.
Zan ba ku sabuwar zuciya, * in sa sabon ruhu a cikinku.
Zan cire zuciyar dutse daga gare ku, * sa'an nan in sa maku zuciyar nama.
Zan sa ruhuna a cikinku, * in sa ku bi ka'idodina, * ku himmanta ga aikata hukuntaina.
Za ku zauna cikin }asar * da na ba kakanninku.
Za ku zama mutanena, * ni kuma in zama Allahnku."
Habakuk 3:2-4,13a,15-19
Yahweh, na ji labarinka, * Yahweh, ayyukanka sun ba ni tsoro.
Ka maimaita su a zamaninmu, * a kwanakinmu ka sanar da su! * Duk da fushinka, ka tuna da yin jin}ai.
Daga Teman Allah ke fitowa, * daga Dutsen Faran Tsattsarkan nan ke tahowa.
[aukakarsa ta rufe sammai, * duniya kuwa ta cika da girmansa.
{yallinsa yana annuri kamar hasken rana, * wal}iyoyi na fitowa daga hannuwansa, * can ne ma~oyin ikonsa...
Ka fito saboda ceton jama'arka, * saboda ceton shaffafen sarkinka...
Da dawakanka ka tattake teku * da haukan ruwa mai }arfi.
Da na ji, sai jikina ya yi rawa, * le~unana suka raurawa,
}asusuwana suka rabke, * }afafuna suka girgiza.
Amma da kwanciyar rai ina jiran masifar * da za ta auko wa wa]anda suka kawo mana ya}i.
Ko da yake itacen ~aure bai yi toho ba, * ba kuma 'ya'ya a kuringar inabi,
zaitun kuma bai ba da amfani ba, * gonaki ba su ba da abinci ba,
tumaki sun ~ace daga garke, * ba kuma shanu a turaku,
duk da haka zan yi farinciki da Yahweh, * in yi murna da Allah Macecina.
Yahweh Ubangijina shi ne }arfina, * yana sa in yi tsalle kamar barewa, * yana kuma bishe ni zuwa
kan duwatsu.
Ishaya 2:2-5
A kwanaki masu zuwa, * dutsen gidan Yahweh zai kafu
bisa sauran duwatsu, * zai fi dukan tuddai tsawo.
Dukan al'ummai za su malalo gare shi, * mutane masu yawa za su zo, su ce:
"Bari mu je dutsen Yahweh, * zuwa gidan Allah na Yakubu,
don ya koya mana hanyoyinsa, * mu kuwa bi labobinsa.
Domin dokokinsa na fitowa daga Sihiyona, * maganar Yahweh kuwa daga Urushalima.
Zai hukunta tsakanin al'ummai, * zai shari'anta mutane masu yawa.
Za su na]e takubbansu su zama garemani, * masunsu ma su zama laujuna.
Al'umma ba za ta yi ya}i da wata al'umma ba, * ba za su }ara koyon ya}i ba.
Gidan Yakubu, zo, * mu yi tafiya da hasken Yahweh.
Ishaya 12:1-6
Ina yabonka, Yahweh, ko da yake ka yi fushi da ni, * gama fushinka ya wuce, ka yi mani ta'aziya.
Hakika, Allah ne Macecina, * ina da sazuciya, bana tsoro.
Yahweh }arfina ne, ina yabonsa, * Yahweh ne wanda ya cece ni.
A ranan nan za ku jawo ruwa da farinciki * daga idon ruwan ceto,
kuna cewa: "Ku gode wa Yahweh, * ku yi kirarin sunansa.
Ku sanar wa al'ummai al'ajibansa, * ku bayyana yadda sunansa yake da girma.
Ku raira wa}a ga Yahweh saboda manyan ayyukan da ya yi, * bari dukan duniya ta ji labarin.
Mazaunan Sihiyona, ku yi sowa da wa}a, * domin Tsattsarkan nan na Isra'ila girma gare shi a
cikinku.
Ishaya 26:1-4,7-9,12
Muna da birni }a}}arfa, * garunsa da ganuwarsa na tsare mu.
Ku bu]e }ofofinsa, * a bar al'umma mai gaskiya ta shiga.
Suna kiyaye aminci, * aniyarsu ta tabbata.
Kana ba su cikakkiyar salama, * domin sun dogara gare ka.
Ku dogara ga Yahweh har abada, * domin Yahweh madauwamin Dutse ne...
Hanyar mai gaskiya daidai take, * kana mai da labinsa bai ]aya sumul.
I, ta bin hanyar hukuntanka, * Yahweh, muna sa zuciya gare ka.
Sunanka da shahararka, * su ne abin da muke marmari.
Raina yana marmarinka da dare, * ruhuna a cikina yana begenka.
Gama da hukuntanka suka zo duniya, * mazaunanta sun koyi gaskiya...
Yahweh, kā }addara mana salama, * domin dukan ayyukanmu, kai ne ka yi su.
Ishaya 33:13-16
Ku da ke nesa, ku ji abin da na yi, * ku da ke kusa, ku gane ikona!
A Sihiyona masu zunubi ke firgita, * makyarkyata ta kama marasa ibada, suka ce:
"Wanene daga cikinmu zai iya zama da wutan nan mai cinyewa? * Wanene daga cikinmu zai iya zama da dauwamiyyar gobara?"
Wanda ya bi adalci, ya yi maganar gaskiya, * ya }i ku]in cuta,
ya hana hannuwansa kar~ar toshi, * ya toshe kunnuwansa ga maganar kisan kai, * ya rufe idanunsa ga muguwar dabara,
wannan zai zauna a wurin mai sama, * mafakar duwatsu matserarsa ce.
Za a kai masa abincinsa, * ruwan shansa ba zai }are ba.
Ishaya 38:10-14,17b-20
Na ce, "A ga~ar }arfina * ina ta }aura.
An sanya ni a }ofofin Shawol * sauran rayuwata."
Na ce, "Ba zan }ara ganin Yahweh * a duniyar masu rai ba.
Ba zan }ara ganin mutun * gun mazaunan Gidan Hutu ba."
An tum~uke ]akina, an na]e shi * an ]aukan mani shi kamar alfarwar makiyayi.
Kamar masa}i kā na]e rayuwata, * kā yanke ta daga gindin saa.
Da rana da dare kana tsananta mani, * ina ta kuka dukan dare.
Kamar zakin da ke kakkarya }asusuwana, * kana tsananta mani dukan yini.
Ina kuka da ~acin rai kamar tsattsewa, * kamar kurciya ina ta yin wa}ar makoki.
Idanuna na duban sama da gajiya, * ya Ubangiji, ina shan wahala, ka lura da ni...
Kā hana raina * shiga Ramin Halaka.
Kā jefa dukan zunubaina * a bayanka.
Gama Shawol ba za ta gode maka ba, * Mutuwa ma ba za ta yabe ka.
Masu gangara wa Kabari * ba su jiran tausayinka.
Sai dai masu rai ne za su yabe ka, * kamar yadda nike yi yau.
Uba zai fa]i * wa 'ya'yansa amincinka.
Yahweh, ka cece mu, * za mu kuwa yi maka wa}a
dukan kwanakin rayuwarmu * a gidan Yahweh.
Ishaya 40:10-17
Ga shi, Ubangiji Yahweh na zuwa da iko, * yana mulki da }arfin dantsensa.
Ya rigaya ya sami lada, * yana da amfanin aikinsa.
Kamar makyayi ne yana kiwon garkensa, * yana tattara 'yan raguna da hannuwansa,
yana rungumarsu a }irjinsa, * yana bi da tumaki kuma.
Wa ya ta~a }irga yawan ruwan teku da hannunsa, * ko ya auna sararin sama da tafinsa?
Wa ya ta~a }irga yawan }asa da buhu, * ko ya auna nauyin duwatsu a ma'auni da tuddai da mizani?
Wa ya ta~a auna ruhun Yahweh, * ko ya zama mashawarcinsa mai ba shi labari?
Wa ya ta~a shawarta don ya fahimce shi, * ya kuwa koya masa hanyar hukunci,
ya koya masa ilimi, * ya nuna masa hanyar fahimi?
A gare shi, al'ummai kamar ]igon ruwa ne a bokiti, * ko }ura bisa ma'auni, * garuruwan da ke ga~ar teku ba su fi toka nauyi ba.
Kurmin Labanan baya da isasshen icen wuta, * ko dabbobin da ake bukata don baikon }onawa.
Dukan al'ummai ba kome ba ne a gare shi, * banza a banza ne gunshi.
Ishaya 42:10-16
Ku raira sabuwar wa}a ga Yahweh, * har bangon duniya ku yabe shi,
ku masu tafiya a kan teku da duk da ke cikinsa, * }asashen da ke ga~ar teku da mazaunansu.
Ku ta da murya, ku }auyukan daji, * da sansanan mutanen Kedar kuma!
Ku yi sowa, ku mazaunan garin Dutse, * ku yi kururuwa daga }wan}olin duwatsu!
Ku yi shelar ]aukakar Yahweh, * ku yabe shi da mutanen da ke gefen teku!
Yahweh na fita kamar jarumi, * kamar maya}i yana ta da aniyarsa.
Yana gunzar kirarin ya}i, * yana kai wa magabtansa hari, yana cewa:
"Na da]e ina yin shiru, * ina ha}uri ba tare da magana ba.
Amma yanzu ina kamar macen da ke na}udda, * ina }ugi da nishi da haki.
Zan lalatar da duwatsu da tuddai, * in busar da dukan ciyawarsu.
Zan mai da kwaruruka hamada, * in busar da fadamu.
Sa'annan zan yi wa mutanena makafi jagora * a hanyoyin da ba su ta~a bi ba.
A kan labunan da ba su sani ba * zan bi da su.
Zan sa duhu ya zama haske a gabansu, * karkatacciyar hanya ta zama daidai.
Ishaya 45:15-25
Lalle, kai ne ~oyayyen Allah, * ya Allah na Isra'ila Maceci.
Masu yin gumaka * sun kunyata, sun sha }as}anci,
dukansu tare, * sun zama abin kunya.
Amma ceton Isra'ila daga wurin Yahweh yake, * dauwamammen ceto ne.
Ba za su kunyata ko su sha }as}anci ba * a zamanai duka nan gaba.
I, Yahweh ne, * Mahallicin sama,
Allah ne, * wanda ya shata }asa, ya yi ta, ya kafa ta.
Bai halicce ta hamada ba, * amma wurin zaman mutane.
In ji shi, "Ni ne Yahweh, * ba wani Allah.
Ba a ~oye na yi magana ba, * ko a duhun lungun duniya.
Ban ta~a cewa da jikokin Yakubu, * 'Ku neme ni a hamada' ba.
Amma ni, Yahweh, ina fa]in gaskiya, * ina sanar da abin da ke daidai.
Ku tattaru, ku zo wuri guda, * ku masu tsira ta gudun hijira.
Ba su san kome ba, * su da ke ]aukar gumakansu na ice,
suna addu'a ga allolin * da ba su iya yin ceto.
Bari su yi magana, su gabatar da matsalarsu, * su shawarci juna.
Wanene ya sanar da abin da zai faru tun dā, * ya kuma yi annabci tuntuni?
Ashe, ba ni ba ne, * Yahweh Allah, * da ba wani sai ni?
Ba Allah na gaskiya, * mai yin ceto, sai ni.
Ku juyo gare ni don ku ku~uta, * ya mutanen ko'ina a duniya,
domin ni ne Allah, * ba wani.
Na yi rantsuwa da kaina, * na fa]i gaskiya, * ba canjin abin da na }addara:
Gwiwar kowa za ta dur}usa a gabana, * kowa zai yi shahada, cewa:
'Daga Yahweh ne * nasara da iko ke zuwa.'"
Amma duk masu yi masa tawaye * za su zo gabansa da kunya.
Ta wurin Yahweh dukan jikokin Isra'ila * za su sami nasara da ]aukaka.
Ishaya 61:10- 62:5
Ina farinciki }warai da Yahweh, * na yi murna da Allahna.
Domin ya suturce ni da rigar ceto, * ya sa mayafin nasara a kaina.
Ina kamar angon da ya sa rawani, * kamar amaryar da ta sa adonta.
Kamar yadda }asa ke fitad da tohonta, * lambu kuma ke tsirad da yabanya,
haka Yahweh zai sa gaskiya da yabo * su tsira a gaban dukan al'ummai.
Ba zan yi shiru a kan Sihiyona ba, * ba kuwa zan bebance game da Urushalima ba,
sai cetonta ya fito kamar haske, * nasararta kuma ta haskaka kamar fitila.
Al'ummai za su ga nasararki, * dukan sarakunansu kuma ]aukakarki.
Za a kira ki da sabon suna, * wanda bakin Yahweh zai ra]a.
Za ki zama kambin ]aukaka a hannunYahweh, * da rawanin mulki a hannun Allahnki.
Ba za a }ara kiranki "Korarriya" ba, * ko }asarki "Kufai",
Amma za a kira ki "aunatacciya", * da }asarki "Amarya".
Gama Yahweh na jin da]inki, * don yana auren }asarki.
Kamar yadda saurayi ke auren matarsa, * haka Mai Gininki zai aure ki.
Kamar yadda ango ke murna da amaryarsa, * haka Allahnki zai yi murna da ke.
Ishaya 66:10-14
Ku yi murna tare da Urushalima, * duk masu sonta, ku yi farinciki tare da ita!
Ku yi murna tare da ita yanzu, * dukanku da kuka yi makoki dominta!
Yanzu ku sha, ku }oshi * daga mamanta na ta'aziya.
Yanzu ku sha, ku ji da]i * daga }irjinta mai yawan nono.
Gama, in ji Yahweh, * "Yanzu ina sa salama ta malalo mata kamar kogi, * da wadatar al'ummai kamar rigyawa.
Za ta goye ku, ta yi renonku, * za ta kuma rungume ku a }irjinta.
Kamar yadda uwa ke ta'aziyar yaronta, * haka ni zan yi ta'aziyarku, * za ku ta'azantu a Urushalima.
Da kuka ga wannan zuciyarku za ta faranta, * jikunanku kuma za su yi yabanya kamar ciyawa.
Irmiya 14:17-21
Idanuna suna zub da hawaye * dare da rana,ba denawa,
saboda babbar masifar da ta faru * ga budurwar da ke jama'ata, * sai ta raunana }warai.
Idan na tafi cikin saura, * sai in ga wa]anda aka kashe da takobi.
Idan na shiga birni, * sai in ga wa]anda ke fama da yunwa.
Har annabi da firist * suna yawon neman abinci inda ba su san kowa ba.
Ka }i Yahuda ke nan ]ungum? * ranka kuma yana jin }yamar Sihiyona ne?
Me ya sa ka buge mu, * har da ba za mu iya warkewa ba?
Muna zuba ido ga samun salama, * amma ba wani alheri da ya zo.
Muna sa zuciya ga warkewa, * amma sai razana.
Yahweh, mun san muguntar da muka yi, * da wadda kakanninmu suka yi, * gama mun yi maka zunubi.
Saboda darajar sunanka, kada ka yashe mu, * kada kuma ka rena Sihiyona, kursiyin ]aukakarka.
Ka tuna da yarjejeniyar da ka yi mana, * kada ka ta da ita.
Irmiya 31:10-14
Ku ce: "Wanda ya warwatsa Isra'ila zai tattaro shi, * zai kiyaye shi kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa."
Gama Yahweh ya fanshi Yakubu, * ya ciro shi daga hannun da ya fi shi }arfi.
Za su zo su yi wa}a a bisa }wan}olin Sihiyona, * za su gudano ga alheran Yahweh,
ga hatsi da abinshan inabi da mai, * ga 'yan raguna da na shanu.
Rayuwarsu za ta zama kamar lambu, * ba za su }ara yin yaushi ba.
'Yan mata za su yi rawa da farinciki, * samari da tsofaffi za su yi murna.
Zan mai da makokinsu ya zama murna, * in ta'azantar da su, in ba su farinciki maimakon ba}inciki.
Zan wadaci firistoci da abinci mai yawa, * jama'ata kuma za su }oshi da alherina.
Bayahudiya 16:1-2,13-16
Ku soma yi wa Allahna wa}a da tambura, * ku yi wa Yahweh yabo da kuge.
Ku raira masa sabuwar wa}a mana, * ku ]aukaka shi, ku kuma kira bisa sunansa.
Gama Allah mai tattake ya}e-ya}e, * shi ne Yahweh...
Ai, dole in raira wa Allahna sabuwar wa}a., * Yahweh, ai, kai mai girma ne da ]aukaka, * mai tsananin iko, ba mai iya karawa da kai.
Ka sa dukan halittunka su yi maka hidima, * gama magana kawai ka yi, sai suka wanzu.
Kai ne ka aiko da numfashinka, ka halitta su, * ai, ba mai iya yin jayayya da kalmarka.
Gama ko da an jijjige gindin tsaunuka da zurfin tekuna, ko da duk duwatsu sun narke kamar dano a gabanka,
ga masu tsoronka * za ka nuna jin}ai.
Gama kowace irin hadaya mai }anshi }aramar aba ce, * haka ma hadayun }onawa masu kitse.
Amma duk mai tsoron Yahweh, * shi ne mai girma har abada.
Hikima 9:1-6, 9-11
Ya Allah na kakannina, Ubangijin jinai, * wanda ka halicci kome ta kalmarka,
ta hikimarka ka sifanta mutun, * don ya mallaki abubuwan da ka halitta,
ya mallaki duniya da tsarki da adalci, * ya zartad da shari'a da adalcin zuciya,
ka ba ni hikimar da ke kewaye da kursiyinka, * kada ma ka ware ni daga cikin 'ya'yanka,
gama ni bawanka ne * kamar yadda iyayena suke dā,
mutun ne kuma, ina da kwanakin rai 'yan ka]an, * na kasa gane shari'a da ka'idodinka.
Ko da ]an adan ya zama cikakke, * in ya rasa hikimarka zai fā]i ba nauyi...
A wurinka hikima take wadda ta san aikinka, * a kan idanunta ne ma lokacin da ka halicci duniya,
ta san abin da ke faranta maka rai, * da kuma abin da ya wajaba a bi cikin dokokinka.
Sai ka kwararo ta daga sammanka masu tsarki, * ka ma aiko ta daga kursiyin ]aukakarka,
don ta zauna da ni, ta yi aiki a cikina, * ai, ta haka ne zan san abin da ke daidai a gabanka.
Gama ita ta sani, ta kuma gane dukan kome, * za ta kāre ni da himma a cikin aikina, * ta bi da ni
da ]aukakarta.
Sirak 36:1-5,10-13
Ka cece mu, ya Allah na dukan halitta, * ka sa sauran al'ummai su ji tsoronka.
Ka nuna wa ma}wabtan al'ummai }arfi, * domin su ga ikonka zahiri.
Yadda ka hore mu domin ka nuna masu tsarkinka, * ka hore su, su ma, domin ka nuna mana ]aukakarka.
Ka sa su san ka, yadda muka san ka, * su sani, ba wani Allah sai dai kai.
Ka koma wa aikinka na al'ajabi, ka yi sababbin alamu, * tashi, ka gwada dantsenka....
Ka tara dukan kabilan Yakubu, * don su gaji }asarsu, kamar yadda yake a dā.
Ka yi jin}ai a kan al'ummar da ake kira da sunanka, * a kan Isra'ila wanda ka kira ]an farinka.
Ka ji }an tsattsarkan birninka, * Urushalima, mazaunin zatinka.
Ka cika Sihiyona da darajarka mai girma, * Haikalinka kuma da ]aukakarka.
Tobi 13:2-8
Yabo ga Allah wanda ke raye har abada, * gama mulkinsa ya tabbata har abada!
Yana raunanawa, yana yin jin}ai, * yana aikawa da mutane Zurfafan Lahira,
ya kuma zaro su daga babbar halaka, * ai, ba mai iya ku~uta daga hannunsa.
Ku yabe shi a gaban al'ummai mana, ku Isra'ilawa, * ai, ko da ya yi ]ai]ai da ku a tsakaninsu, * a can ma ya nuna muku ikonsa a fili.
Ku ]aukaka shi a gaban dukan mutane, * gama shi ne Yahweh Allahnmu, * shi ubanmu ne da Allahnmu, har abada abadin.
Ko da yake ya hore ku a kan zunubanku, * ai, zai ma ji tausayin dukanku.
Zai tattaro ku gu ]aya daga sauran al'ummai, * daga duk inda aka yi ]ai]ai da ku a dā.
In dai kun juya gare shi da dukan zuciyarku, * kuna aikata aikin gaskiya a gabansa,
Sa'annan zai juyo gare ku, shi ma, * ba kuma zai }ara ~oye muku fuska ba.
Ku dubi dai irin abin kirkin da ya yi muku, * ku gode masa mana, kai jama'a!
Ku yabi Ubangijin adalci, * ku kuma ]aukaka Sarkin dukan zamanai!
Ai, ni ma nakan yi wa}ar yabonsa * a lokacin da nake bawan ya}i a wani gari.
Na sanar da ikonsa da girmansa a fili * ga al'ummar da take yin sa~o.
Ai, ku masu sa~o, sai ku juya gunsa, * ku dai kasance da hali mai kyau.
Lalle zai yi muku alheri, * ya kuma ji tausayinku.
Ni ma ina ]aukaka Allah, * raina kuma yana yin fari fat da Sarkin nan na Sama.
Bari girmansa ya zauna a bakin dukan mutane, * a yi wa}ar yabonsa a Urushalima.
Tobi 13:8-14
Bari girmansa ya zauna a bakin dukan mutane, * a yi wa}ar yabonsa a Urushalima.
Ya Urushalima, birni mai tsarki, * Allah ya raunana ki a kan gumakan da kika yi, * amma duk da haka zai ji tausayin 'ya'yanki, adalai.
Ki gode wa Allah saboda alherinsa, * ki yabi Sarkin dukan zamanai!
Domin za ki yi farinciki * da ganin an sāke gina masujadarsa a cikinki.
Zai kuma dawo miki da bayin ya}inki, * ya ta'azanta su a cikinki.
Dukan wa]anda ke ba}inciki zai }aunace su a cikinki, * har dukan zamanai masu zuwa.
Ai, hasken haske zai haskaka * a kan duk sashe na duniya.
Kabilai za su bangazo gare ki daga wurare masu nisa, * daga wannan bangon duniya zuwa wancan, * domin su ji labarin alherin da Yahweh ya yi miki,
suna da kyautai a hannunsu * domin Sarkin Sama.
A cikinki, tsara za ta bi tsara, * suna bayyana matu}ar farincikinsu a kanki.
Har ga 'yan zamanin nan na gaba, * kowa zai san Allah ya za~e ki.
Yanzu dai, sai ki yi murna * da 'ya'yanki adalai,
gama za a tara su duka a gu ]aya, * su yabi Ubangijin dukan zamanai.
Albarka ta tabbata gun masu }aunarki, * da wa]anda ke na'am da zaman alamarki.
Masu albarka ne kuma su da suka yi makoki * a kan dukan wahalarki.
Filibiyawa 2:6-11
Ko da yake surar Allah yake, * Yesu bai mai da daidaitakan nan tasa da Allah * abar karabkiya ba,
sai ma ya mai da kansa baya matu}a * ta ]aukar surar bawa, * da kuma kasancewa da kamannin ]an'adan.
Da ya bayyana da siffar mutum, * sai ya }as}antad da kansa ta yin biyayya,
har wadda ta kai shi ga mutuwa, * mutuwar ma ta kan gicciye.
Saboda haka ne kuma Allah ya ]aukaka shi mafificiyar ]aukaka, * kuma ya yi masa baiwa da sunan nan * da ke birbishin kowane suna,
don dai kowace gwiwa sai ta rusuna * wa sunan nan na Yesu, * a sama da }asa, da kuma can }ar}ashin }asa,
kowane harshe kuma ya yarda cewa * Yesu Almasihu Ubangiji ne, * don ]aukaka Allah Uba.
Wahayin Yahaya 19:1,5-8
Halelu-Yah! Yin ceto, da ]aukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu, Halelu-Yah!
don hukuncinsa daidai yake, kuma na gaskiya ne. Halelu-Yah, Halelu-Yah!
Halelu-Yah! Ku yabi Allahmmu, ya ku bayinsa, Halelu-Yah!
ku da ke jin tsoronsa, yaro da babba. Halelu-Yah, Halelu-Yah!
Halelu-Yah! Gama Ubangiji Allahmmu Ma]aukaki shi ke mulki, Halelu-Yah!
mu yi murna da farinciki matu}a, mu kuma ]aukaka shi. Halelu-Yah, Halelu-Yah!
Halelu-Yah! Don bikin [an Ragon nan ya zo, Halelu-Yah!
amaryatasa kuma ta kintsa. Halelu-Yah, Halelu-Yah!
Halelu-Yah! An yarje mata ta sa tufafi lallausa Halelu-Yah!
mai ]aukar ido, mai tsabta. Halelu-Yah, Halelu-Yah!
Halelu-Yah! [aukaka ga Uba da ga [a da ga Ruhu Mai Tsarki, Halelu-Yah!
yanzu da har abada. Halelu-Yah, Halelu-Yah!
Afisawa 1:3-10
Yabo ya tabbata ga Allah da Uba * na Ubangijimmu Yesu Almasihu!
Gama ya yi mana albarka da kowace albarka mai ruhaniya * a mu}aman sama * ta kan Almasihu.
Allah ya za~e mu ta kansa * tun ba a halicci duniya ba * mu zama tsarkaka, marasa aibu a gabansa.
Ta }aunarsa ya }addara mu *ga zama 'ya'yansa
ta kan Yesu Almasihu * bisa nufinsa na alheri,
don mu yabi ]aukakar alherinsa * wanda ya ba mu kyauta hannu sake ta kan aunataccensa.
Ta gare shi ne muka sami fansa * albarkacin jininsa, * watau yafewar laifuffukammu,
bisa yalwar alherin Allah, * wanda ya yi mana falala.
Da matu}ar hikima da basira, * ya sanasshe mu zuzzurfan al'amarin nufinsa
bisa kyakkyawan nufinsa * da ya bayyana game da Almasihu.
Duk wannan shiri ne, don a cikar lokaci * a harha]a dukan abubuwa ta kan Almasihu,
watau, abubuwan da ke sama * da abubuwan da ke }asa.
Wahayin Yahaya 4:11; 5:9-10,12
Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahmmu, * ka sami ]aukaka da girma da iko.
Don kai ne ka halicci dukan abubuwa, * da nufinka ne suka kansance kuma aka halicce su...
[an Ragon Allah, macancanci ne kai * ka ]auki littafin nan, * ka ~am~are hatimansa.
Domin dā an kashe ka, * kuma ka fanso wa Allah mutane ta jininka * daga kowace kabila, da kowane harshe, da kowace jama'a, da kowace al'umma.
Ka mai da su jama'a, * kuma firistocin Allahmmu, * suna kuwa mulki a duniya...
Macancanci ne [an Ragon nan da aka yanka * ya sami iko,
da wadata, da hikima, da }arfi, * da girma, da ]aukaka, da yabo.
Kolasiyawa 1:12-20
Ku gode wa Uba, * wanda ya maishe ku isa samun rabo
cikin gadon tsarkakan * da ke cikin haske.
Ya tsamo mu daga mulkin duhu, * ya maishe mu ga mulkin }aunataccen Ðansa,
wanda ta gare shi ne muka sami fansa, * watau gafarar zunubammu.
Shi ne surar Allah mara ganuwa, * Magaji ne tun ba a halicci kome ba,
Don ta gare shi ne aka halicci dukan kome, * abubuwan da ke sama da abubuwan da ke }asa, * masu ganuwa da marasa ganuwa,
ko manyan mala'iku, ko masu mulki, * ko masarautu, ko masu iko,
watau dukan abubuwa an halicce su ne ta kansa, * kuma shi ne makomatasu.
Shi adimi ne gaba da kome, * kuma dukan abubuwa shi ke ri}e da su.
Shi ne Kai ga jikin nan, watau ikiliziya, * shi ne Tushe,
Na Farko cikin masu tashi daga matattu, * don ta kowane abu ya zama shi ne mafifici.
A gare shi dukan cikar Allah ta tabbata, * don Allah na farinciki da haka,
da nufin ta kansa * Allah ya sada dukan abubuwa da shi kansa,
na }asa ko na sama, * yana }ulla aminci ta jininsa na gicciye.
Wahayin Yahaya 11:17-18; 12:10b-12a
Mun gode maka, ya Ubangiji Allah, Ma]aukaki * wanda yake shi ne a yanzu, shi ne kuma a dā,
saboda ka ]auki ikonka mai girma, * kana mulki.
Al'ummai sun husata, * hushinka kuwa ya sauko, * lokaci ya yi da za a yi wa matattu shari'a,
a kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako, * da masu jin tsoron sunanka, * yaro da babba...
Yanzu fa ceto, da }arfi, da mulki na Allahmmu, * da kuma ikon Almasihunsa sun bayyana.
Don an jefa mai saran 'yan'uwammu }asa, * shi da ke saransu dare da rana a gun Allahmmu.
Sun kuwa yi nasara da shi * albarkacin jinin [an Ragon nan, * da kuma albarkacin maganad da suka shaida,
don ba su yi tattalin ransu ba, * har abin ya kai su ga kisa.
Saboda haka sai ku yi farinciki, ya ku sammai, * da ku mazauna ciki!
Wahayin Yahaya 15:3-4
Ayyukanka manya-manya ne, kuma masu ban mamaki, * ya Ubangiji Allah Ma]aukaki!
Hanyoyinka na gaskiya ne, kuma daidai suke, * ya Sarkin al'ummai.
Wanene ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, * ya kuma ]aukaka sunanka? * domin kai ka]ai ne tsattsarka.
Dukan al'ummai za su zo * su yi maka sujada,
don hukuncinka na gaskiya * yā bayyana.
1 Bitrus 2:21-25
Almasihu ya sha wuya dominku, * ya bar muku misali * ku bi hanyarsa.
Bai ta~a yin laifi ba faufau, * ba a kuwa ta~a jin yaudara a bakinsa ba.
Da aka zage shi * bai rama ba,
da ya sha wuya kuwa bai yi }wafa ba, * sai dai ya dogara ga wannan Mai shari'ar gaskiya.
Shi da kansa ya ]auke zunubammu * a jika a kan gungume,
don mu fita sha'anin zunubi ]ungum, * mu yi zaman aikin gaskiya.
Da raunukansa ne * aka warkad da ku.
Dā kun sangarce kamar tumaki, * amma yanzu kun dawo ga Makiyayi, * kuma Mai kula da
rayukanku.
Luka 1:47-55 Wa}ar Maryamu
Zuciyata na ]aukaka shi Ubangiji, * Allah Macecina * da shi ruhuna yake ta farinciki.
Domin fa shi ya dubi }asancinta ne baiwa tasa, * ai ga shi jama'a ta dukan zamani * mubarika ce za su ce mani nan gaba.
Domin fa shi da ya ke yana Mai iko, * ai manya-manyan al'amurra yai mani, * sunansa ko labudda tsattsarka yake.
Daga zamani har dai zuwa wani zamani, * tausansa na ga wa]anda ke tsoro nasa.
Al'amari babba da }arfinsa ya yi, * ya watsa duk mutakabbirai sun watse.
Ya firfitad da sarakuna a sarauta, * ya ]aukaka masu zaman }as}anci.
Mayunwata ya yalwata da abubuwan alheri, * ya sallame su da babu, masu wadata.
Ya taimaka wa baransa Isra'ila, * domin yana tune dai da yin rahama tasa.
Ita ya yi alkawari ga kakannimmu, * tutur ga Ibrahim da duk zuriya tasa.
Luka 1:68-79 Wa}ar Zakariya
Ubangiji Allah na Isra'ila * a gare shi ne lalle yabo ke tabbata, * don ya kula, ya fanshi ma jama'a tasa.
Ya ta da Maceci mai iko domin mu, * daga zuriya ta baransa Dauda,
yadda a tuntuni ya fa]a fa ta bakunan * su annabawa nasa tsarkakan nan:
ya cece mu a gun su abokan gabammu, * har ma a hannun dukan ma}iyammu.
Don nuna rahama ne ga kakannimmu, * ya tuna da alkawari nasa tsattsarkan nan.
Shi ne rantsuwan nan wadda yai wa Ubammu Ibrahimu, * y cece mu gun su abokan gabammu,
ya ba mu baiwa don mu dai bauta masa, * a gabansa ba a cikin halin tsoro ba ne,
sai dai cikin tsarki da halin gaskiya, * dukan iyakar kwanakin nan namu.
Kai kuma, yaro, za a kira ka annabi ne na Ma]aukaki, * za ka riga Ubangiji gaba, ka shisshirya hanyoyi nasa,
ka sanad da su cetonsu su jama'a tasa, * watau na samun gafarar zunubai nasu.
Saboda tsananin rahamar Allahmmu, * daga can sama ne hasken alfijir zai keto mana,
har ya haskaka su na zaune can cikin duhu a bakin halaka, * har ma ya dai bishe mu hanyar lafiya.
Luka 2:29-32 Wa}ar Simiyan
Yanzu kam ya Mamallaki, * sai ka sallami bawanka lafiya, * bisa fa]an nan da ka fa]a.
Don na ga cetonka zahiri, * da ka shirya a gaban kabilun nan duka,
Haske mai yi wa sauran al'ummai bu]i * abin kuma ]aukaka jama'arka Isra'ila.